31 Agusta 2020 - 13:36
​ Isra’ila : An Shiga Mako Na Goma A Zanga Zangar Kin Jinin Netanyahu

Rahotanni daga Isra’ila na cewa, an kwashe daren jiya ana ta zanga zangar kin jinin firaminista Benjamin Netanyahu a sassa daban daban na

ABNA24 : Bayanai sun ce zanga zangar na ci gaba da yaduwa inda ko a jiya dubban mutane ne suka taru gaban gidan firaministan kasar inda suke bukatarsa da ya yi murabus, kafin daga bisani ‘yan sanda su bukace su fice daga wajen cikin lumana ba tare da kuwacce kuwace ba.

Wannan dai shi ne mako na goma a jere da ake irin wannan zanga zangar.

Masu zanga zangar dai na bukatar Netanyahu, ya yi murabus saboda zargin cin hanci da rashawa, da kuma gazawa wajen dakile yaduwar cutar korona.

342/